Allah Yayi Alkawarin Bayar Da Nasara Ga Wanda Yayi Hakuri Da Kaddararsa, Mai Kyau Ko Marar Kyau, Daga Imam Murtadha GusauDukkanin kyakkyawan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah Madaukaki, taimakonsa da gafararsa muke nema; kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda kuma ya batar to babu mai shiryar da shi.
“Shine (Allah) wanda yayi halitta, kuma ya daidaita ta, kuma shine wanda ya kaddara abubuwa, kuma ya shiryar da su.”Ya ku bayin Allah masu daraja! A takaice dai ayoyin da suke tabbatar da wannan muhimmin rukuni na imani da kaddarar Allah da hukuncinsa, sun fi a kirga. Don haka, tilas ne ga duk wani Musulmi, wanda ya amsa sunansa na Musulunci, ya yarda cewa babu wani abu da zai faru cikin mulkin Allah, wanda sai daga baya Allah zai san shi. A’a, Allah ya rigaya, yasan komai tun fil-azal, kuma ya rubuta shi a allon kaddara, wanda yake wurinsa (wato lauhil mahfuz), kamar yadda yazo a cikin ingantaccen Hadisi, kuma kamar yadda Allah Madaukaki yake cewa:“Lallai hakan, yana cikin littafi, lallai hakan mai sauki ne a wurin Allah.
Ya ku ‘yan uwana! Ku sani, babu tilas ga dan Adam akan ayyukansa, a cikin akida ta Musulunci. Kuma mutum yana da dama da kuma zabi, ya aikata abin da ya ga dama, kamar yadda Allah Madaukaki yake cewa:“Kuma mun shiryar da shi hanyoyi biyu (wato na alkhairi da na sharri).” 4. Halittar Allah ga abubuwa, da samar da su da kudurarsa cikakkiya. Allah shine ya halicci kowane mai aiki da duk aikinsa, da duk wani mai motsi da motsinsa, da duk wani mai sukuni da sukuninsa.“Allah yana nan, lokacin da babu wani abu tare da shi. Kuma al’arshinsa ya kasance a kan ruwa. Kuma ya rubuta komai a cikn lauhul mahfuz. Kuma ya halicci sammai da kasa.”
“إن عِظَمَ الجزاءِ مع عِظَمِ البلاءِ، وإن الله تعالى إذا أحب قوما ابتلاهم، فمن رَضِيَ فله الرِضا، ومن سَخِطَ فله السُّخْطُ.” “Lallai gwaggwabar lada mai yawa mai tsoka tana tare da girman bala’i da jarabawa, kuma Allah Mai girma da daukaka idan yana son wasu mutane to sai ya jarrabesu; duk wanda ya yarda da jarrabawar Allah, to sai ya sami yardar Allah da nasararsa, kuma duk wanda yayi fushi da kaddarar Allah, to shi ma sai Allah yayi fushi da shi.
Similar News:You can also read news stories similar to this one that we have collected from other news sources.
Source: TheNationNews - 🏆 6. / 69 Read more »
Source: DailyPostNGR - 🏆 11. / 59 Read more »
Source: vanguardngrnews - 🏆 5. / 75 Read more »
Source: NigeriaNewsdesk - 🏆 10. / 63 Read more »
Source: DailyPostNGR - 🏆 11. / 59 Read more »
Source: vanguardngrnews - 🏆 5. / 75 Read more »